Abin da ya sa gwamnoni ba su iya samar wa jama’a ababen more rayuwa –Gwamna Yari

0

Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya ce rashin isassun kudade na kawo wa gwamnnonin jihohi cikar wajen daukar nauyin da ya rataya a wuyan su na samar wa al’ummomin jihar ababen more rayuwa.

Ya ce matsalar isassun kudade na haka wadatuwar ingantattun ayyukan lafiya, hasken lantari, samar da ilmi, gina titina da sauran su.

Ya ce dalili shi ne saboda an takaitar da gwamnoni wajen biyan albashin ma’aikata kawai. Kan haka ne gwamnan ya ce shi ya sa gwamnoni ba su iya yin ayyukan da za a gani a yaba, saboda karancin kudade.

Jaridar Punch ta ruwaito Yari ya yi wannan bayani ga manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, bayan fitowa daga taron gwamnoni suka yi tare da Mukaddashin Shugaban Kasa, a ranar Laraba.

Yari, wanda har ila yau shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, ya ce a rake duba fasalin kudaden da ke shigo wa gwamnati tun daga shekaru 14 da suka gabata, domin a samu matsaya daya tilo a kan mafi karancin albashin ma’aikata.

Har yanzu dai ana ta kiki-kaka a kan tsayayyen mafi karancin albashi, yayin da Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC ta ce sai dai a biya naira 65,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Share.

game da Author