Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da a shigo da tsatstsaurar doka mai tsananin hukunci kan duk wanda ya yi gigin fitar da sakamakon zabe na jabu.
Jega ya yi wannan kiran ne a jiya Laraba, yayin da ya ke jawabi wurin Kasa-da-kasa kan hanyoyin dakile labaran jabu.
Ya ce batun labarai na jabu inda haka kawai wani zai tashi ya kirkiri karya, abin ya na zama barazana kan dimokradiyyar Najeriya.
Daga nan sai ya yi kakkausan kira da cewa ya kamata a gaggauta magance wannan gagarimar matsala, tun kafin ta gagara magancewa.
Jega ya ce irin yadda ake watsa sakamakon zabe na jabu a soshiyal midiya, abin ya munana sosai.
“Don haka akwai matukar bukatar a yi wa wasu dokoki kwaskwarima, domin a shigo da tsauraran hukunci ga masu bayyana sakamakon zabe na jabu.”
Ya ce tunda ga zaben 2019 ya kunno kai, akwai bukatar gaggauta tsaurara dokar.
A na sa bayanin, Shugaban INEC Mahmood Yakubu, ya ce hukumar ta sa ta na ta faman yaki da masu fitar da labarai na karairayi.
Kwamisninan Zabe na Kasa, Okechukwu Ibeanu ne ya wakilci Shugaban INEC.