2019: Dalilin da zai hana dan kabilar Igbo zama shugaban kasa – Okorocha

0

Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, ya bayyana dalilan da ya ce su ne suka sa kujerar shugabancin Najeriya ta zame wa kabilar Igbo tamkar wutsiyar rakumi, wadda ta yi nisa da kasa.

Okorocha ya ce Igbo kabila ce mai tsananin kyashin ‘yan uwanta, sannan sun ciri tuta kwarai wajen kokarin ganin sun dankwafar da ‘yan’uwan ta da aka ga taurarin su na haskawa a duk harkokin da suke ciki.

Wata ruwaya daga jaridar Punch, ta bayyana cewa Okorocha ya yi wadannan kalamai a yayin tattaunawar sa da manema labarai a Fadar Gwamnatin Jihar Imo, Owerri, babban birnin jihar.

Okorocha, wanda a cikin 2003 ya nemi tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APP, amma abin haushi bai samu goyon baya daga yankin sa na kabilar Igbo.

“Su fa kabilar Igbo ba su san ma yadda za su dauki manyan yankin su da muhimmanci ko wata martaba ba.

“A duk lokacin da na fito neman takarar shugaban kasa, ba na fuskantar zagon-kasa daga Arewa, ko yankin Kudu Maso Yamma ko Kudu maso Kudu, sai a yankin kabilar Igbo kadai.”

Ya ce dan kabilar Igbo ba shi da wata kima ga dan uwan sa Igbo.

Shi ya sa duk wani dan kabilar Igbo da ya fito takarar shugaban kasa, ba ya sawa a ran sa cewa ‘yan uwan sa Igbo za su yi masa taron-dangin goyon baya har ya yi nasara. Ba su ganin darajar na su, sun fi ganin darajar na waje. To haka ya ke a cikin jinin su.

“Ka shiga jaridu da soshiyal midiya, duk wulakanci da tozartawa da muzantawar da ake yi wa mutum, za ka ga daga yankin Igbo surutan ke fitowa.”

Share.

game da Author