2019: Buhari ya ziyarci ofishin yakin neman zaben sa

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci ofishin yakin neman zaben sa na 2019 a yau Laraba.

Ofishin wanda ke kan titin Herbert Macaulay Way, a Central area, Abuja, shi ne dai ofishin kamfen din sa na shugaban kasa a zaben 2015.

Cikin wadanda suka take masa baya akwai Shugaban Ma’aikatan Fadar sa, Abba Kyari, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da kuma wasu jami’an gwamnati.

Wadanda suka karbi bakuncin tawagar sun hada da Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Ameachi, wanda shi ne ma ya zagaya da Buhari cikin kowane ofis domin gane wa idon sa yadda aka kayata ofisoshin.

Buhari ya nuna gamsuwa da irin yadda aka gyara ofisoshin sosai, kuma ya gode wa wadanda aka dora wa alhakin gyara ofis din.

Share.

game da Author