2019: Buhari da sauran shugabannin APC za su gana

0

Shugabannin APC sun shirya tsaf domin gudanar da taro Shugabannin Zartaswar Jam’iyyar, na farko tun bayan da Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya fice daga jam’iyyar.

Wata kwakkwarar majiya daga cikin APC ta ce za a yi taron a sakateriyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja da karfe 10 na safiyar Alhamis.

Ana sa ran za a tattauna batutuwan da suka shafi zaben 2019 mai zuwa da ke karatowa, musamman zabukan fidda gwanin jam’iyyar.

Kwamitin Shugabannin Zartaswar dai ya kunshi shugaban kasa, mataimakin sa, gwamnonin APC da shugabannin jam’iyya na jihohi 36.

Akwai kuma Shugaban Majlisar Dattawa nan a Tarayya, tsoffin shugabannin kasa da mataimakan su da ke cikin APC da kuma tsoffin gwamnonin da ke cikin APC a yanzu haka.

PREMIUM TIMES ta ji cewa kafin taron wanda za a gudanar ranar Alhamis, Buhari zai gana da ‘yan jam’iyyar a cikin Fadar Aso Villa a ranar Talata mai zuwa.

Majiya ta kara da cewa za a gudanar da wannan ganawa da Buhari ce da dare, kwanaki biyu kafin taron kwamitin shugabannin zartaswar.

Majiya ta kara tabbatar da cewa taron dai zai yi magana ne kan gangamin zaben fidda gwani na jam’iyyar da za a gudanar cikin watan Satumba mai kamawa.

Ana kuma sa ran za a amince da yin wasu ‘yan canje-canjen ranakun gudanar da zabukan fidda-gwanin jam’iyyar mai mulki.

Share.

game da Author