2019: APC ta karyata sa ranar gudanar da zaben fidda gwani

0

Jam’iyyar APC ta musanta labarin aza ranar zaben fidda gwanin da aka ce ta yi na zabukan 2019 da ke karatowa.

Rahotanni da dama sun nuna cewa APC ta fidar da jadawalin ranakun gudanar da zaben fidda gwani, wanda a baya aka ce za a gudanar tsakanin ranakun 15, 19, 23, 28 ga Satumba, da kuma na shugaban kasa da aka ce za a gudanar a ranar 6 Ga Oktoba, 2018.

Sai dai kuma a cikin wani bayani da Sakataren Riko na APC, Yekini Nabena ya sa wa hannu, ya bayyana cewa APC ba ta aza rana ba, kuma ba ta fitar da wani jadawali ba.

“Wannan jadawali da aka ce APC ce ta fitar da ita, to ta jabu ce, ba gaskiya ba ce. Don haka kowa ya yi watsi da ita kawai. Har yau APC ba ta tsaida rana ba, kuma ba ta fitar da jadawalin ba.

Share.

game da Author