Alhazan Najeriya uku sun rasu a hadarin mota a kusa da Madina

0

Shugaban kula da lafiyar Alhazai na hukumar NAHCON Ibrahim Kana ya tabbatar wa manema labarai cewa wasu alhazai daga jihar Zamfara sun rasu a hadarin mota daga Madina zuwa Makka a safiyar Juma’a.

Alhazan da suka rasu sun hada da Shinkafi Mudi Mallamawa, Abdullahi Jafaru Gidan Sambo,da Abdullahi Shugaba.

An aika da gawarwakin wadannan Alhazai da suka rasu asibitin Sarki Fahad dake Madina, inda sauran wadanda suka ji ciwo aka kwantar dasu a wani asibiti dake kusa da Madinna.

Shugaban kungiyar ‘yan jarida na jihar Zamfara Abdulrazak Kaura da shi ma yanzu haka yana kasar Saudi ya ce dukkan wadanda suka rasu shugabannin jam’iyyar APC ne a kananan hukumomin Zamfara.

” Jafarau Gidan Sambo shine shugaban APC na karamar hukumar Kaura Namoda, Mudi Mallamawa na Shinkafi sannan Abdullahi Shugaba na Karamar hukumar Maru.”

Share.

game da Author