An kama barauniyar da ke yi wa ‘yan acaba tayin alawa, da sun sha sai su mika mata mukulli

0

A yau Alhamis ne rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wata barauniya mai suna Zinatu Abubakar da laifin sace babur.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Gambo Isa ya sanar da haka wa manema labarai a garin Katsina.

Ya ce Zinatu ta hau babur din wani mutum mai suna Gide Wada cewa zai kai ta rukunin gidajen unguwar Rima dake cikin garin Katsina daga Kofar Kaura inda ta tsayar da shi.

” Sai Zinat ta yi wa Wada tayin alewar chakulat yayin da suka fara tafiya ai ko bayan ya gama tsotsan wannan alewar sai ya fara ganin jiri.

” Sanadiyyar haka sai Wada ya tsayar da babur amma kafin ya ankare wasu abokan Zinatu masu suna Abubakar da Chairman suka diran masa inda suka yi korarin kwace babur din da karfin tsiya. Da Wada ya ga bazai iya da su ba sai ya kwantsama ihu nan-nan ko mutane suka kawo masa agaji.

Isa ya ce mutanen sun cafke Zinatu sannan Abubakar da Chairman suka tsere.

Ya ce bincike ya tabbatar musu cewa Zinatu da abokanta na cikin wata kungiyar ‘yan bata gari dake sace wa ‘yan achaba babura kuma an gano sun dade suna aikata wannan ta’asa a Kaduna da Kano.

A karshe Isa ya yi kira ga duk ‘yan achaba da su guji karban abinci daga hunnun mutanen da basu san su ba.

Ya ce rundunar ta fara farautan Abubakar da Chairman don gurfanar da su.

Share.

game da Author