Kwamitin Koli na Jam’iyyar APC ta amince da yin amfani da shirin zaben fidda dan takarar shugaban kasa ne kawai ta hanyar shirin zaben fidda dan takara na duk mai mallakin katin jam’iyya wato (Direct).
Hakan ya biyo bayan sakamakon ganawa ta kwamitin ta yi yau a hedikwatar jam’iyyar dake Abuja.
Kamar yadda aka fitar da sakamakon ganawar, sauran zabukan fidda dan takara zai zamo ta hanyar yin amfani da wakilan jam’iyyar ne kawai, wato deliget, (Indirect).
Idan ba a manta ba da yawa daga cikin musamman sanatoci da ‘yan majalisar tarayya sun koka kan wannan shiri na jam’iyyar cewa idan har za ayi haka to fa zasu tattara kayan su su fice daga jam’iyyar APC.
Babban abin da masu yin fashin baki a harkar siyasa suka aiyana shine, dole a sami baraka idan har ba duka zabukan za a yi amfani da wannan shiri na (Direct) ba domin kuwa kowa ya san yadda gwamnoni a jihohi suka wasa wukaken su don ganin cewa ba a amince da wannan shiri a jihohin su ba.
Gwamnoni ne ke da wakilan jam’iyya, duk wanda ba ya tare da gwamna kenan kashin sa ya bushe.
Yanzu dai majalisar Koli na jam’iyya mai mulki ta rattaba hannu akai, sai dai kuma a jira abin da zai wakana nan gaba.