Shugaban Majalisar dattawa Bukola Saraki ya bayyana ra’ayin sa na yin takarar shugabancin Najeriya a Jam’iyyar PDP.
Saraki ya kaddamar da kan nasa ne a Otel din Sheraton dake Abuja da yake ganawa da wasu matasa ‘yan takara a jam’iyyar.
Idan ba a manta ba Saraki da wasu hasalallun ‘yan jam’iyyar PDP sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a watan jiya.
Jiya Laraba ne tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar na sa fitowa takarar a garin Abuja.
Discussion about this post