Na yi wa matata karyar na mutu saboda yawan tambaya na Kudi da take yi – Magidanci

0

Wani mazaunin kasar Amurka kuma dan kasar Honduras mai suna Danny Gonzalez ya karyata mutuwar sa domin guje wa yawan bani-bani daga wurin matar sa.

Gonzalez na daya daga cikin ‘yan kasar Honduras da iyalen su ke dogaro da su sanadiyyar zaman da suke yi a can kasar Amurka.

Gonzalez ya ce tun da ya koma zama a kasar Amurka matar sa ta zama aljihu da kulum sai dai a zuba masa kudi.

” Duk ranar Asabar matata kan kira ni a waya sannan duk kiran da za ta yi mun na tambayar kudi ne daga nan kuma babu abin da zai sake hada ni da ita.

” Ganin yawan bani-bani din da matata ke yi ya ishe ni sai na dauki wannan mataki na in karyata mutuwa ta.

Ai ko bayan ya aika mata da hotunan sa kwance kamar gwa, sai ko ‘yan uwansa suka rude, suka fara neman yadda za suyi su tabbatar da haka. Jaridu suma basu bar maganar ta wuce haka kawai ba.

Daga baya sai aka gano cewa ashe bai mutu ba yana nan da ran sa lafiya sumul. Matar sa ce kawai ya nemi ya tada wa hankali ko ya huta da tambaya.

Daily Trust ne ta ruwaito wannan labarin.

Share.

game da Author