An cafke wani matashi da ya sace dala 4000 yana bushahar sa a Gombe

0

A yau Laraba ne rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta kama wani matashi dan shekara 19 mai suna Idris Abubakar dauke da dala 4,000.

Kakakin rundunar Mary Malum ta sanar da haka wa manema labarai a garin Gombe inda ta kara da cewa sun kama Abubakar da wadannan dalolin ne, da kuma Naira 21,000,turamen atanfofi biyu, takalma biyu,nauran sauraron sauti,wayar tarho da alewar chakulat bakwai.

Ta ce rundunar ta kama Abubakar ne bayan wani ya kawo musu karan yadda yake ta bushashar sa da kudaden ranar 19 ga watan Agusta a ofishin su.

” Daga nan ne muka fara bibiyar sa a hankali har muka kama shi. Abubakar ya tabbatar mana cewa ya sato kudaden ne a gidan wani dan kasar Lebanon da yake yi wa aiki a garin Kano.

A karshe malum ta ce sun aika wa shashen da ake hukunta masu aikata irin wannan laifi domin ci gaba da bincike.

Share.

game da Author