Hukumar NUC ta tattance kwasakwasai 20 a jami’ar Tarayya dake Kebbi

0

Hukumar jami’o’I ta kasa (NUC) ta tattance kwasakwasai 20 jam’iar gwamnatin tarayya dake Birnin Kebbi, jihar Kebbi.

Jami’in jami’ar Jamilu Magaji ya bayyana haka a wata takardar da ta fito daga ofishin sa inda ya kara da cewa hukumar ta kammala tattance kwaskwasai 12 daga cikin 20 sannan sauran takwas din za ta kammala tattance su bayan shekaru biyu.

Magaji ya ce hukumar ta fara tattance kwaskwasan ne tun a watan Maris sannan bayan watanni hudu ta gabatar da wannan sakamako.

Ya ce cikin kwasakwasai 12 din a aka kammala tattance su sun hada da Accounting, Applied Geophysics, Biochemistry, Business Administration, Computer Science, Demography and Social Statistics, Economics, History and International Studies, Mathematics, Political Science, Sociology da Statistics.

Sannan sauran guda takwas din da ba kammala tattance sune Biology, Chemistry (Industrial), Chemistry (Pure), English Language, Geography, Geology, Microbiology da Physics Electronics.

A karshe shugaban jami’ar Balla Shehu ya yabawa hukumar NUC bisa wannan kokari da ta yi na tantance kwasa-kwasan da ta yi.

Share.

game da Author