Jam’iyyar APC ta jaddada aniyar ta wajen bin umarni da kiyaye dukkan ka’idoji da sharuddan da Hukumar Zabe, INEC ta gindaya yayin gudanar da zabukan fidda gwanin makaman siyasa daban-daban na jam’iyyar da za a yi cikin watan Satumba.
Shugaban jam’iyyar na Kasa, Adams Oshiomhole ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai na Gidan Gwamnati, bayan bayan kammala taron da masu ruwa da tsakin jam’iyyar suka gudanar a Fadar Shugaban Kasa, a Talata da dare.
Ya tabbatar da cewa sun gudanar da taron ne inda suka tattauna batun zabukan fidda gwanin ‘yan takarar jam’iyyar da za a yi a bisa tsarin tantebur da INEC ta fitar a cikin watan Janairu.
Jadawalin ya kunshi zabukan fidda gwanin shugaban kasa, majalisun tarayya da na jihohi, zaben gwamnoni da kuma zabukan FCT.
Jadawalin shirye-shiryen zaben 2019 da INEC ta fitar, ya jaddada cewa lallai kowace jam’iyya ta tabbatar da cewa ta gudanar da zaben fidda gwani tsakanin watan Agusta zuwa 7 Ga Oktoba, 2018.
Don haka sai Oshiomhole ya ce ai ya zama wajabi APC ta bi dokokin da INEC ta shimfida, domin ita ma INEC din, ta tsamo dokokin ne daga cikin kundin tsarin dokokin Najeriya da ke tattare da bayanan shirya zabe.