Dan Najeriya ya rasu a Otel a Makka

0

Wani dan Najeriya ya rasu a hadarin na’urar lifta a wani Otel dake garin Makka.

Jami’in dake kula da fannin kiwon lafiyar Alhazai na hukumar NAHCON, Ibrahim Kana ya tabbatar da haka sannan ya ce a zuwa yanzu Alhazan Najeriya 4 kenan suka rasu a aikin Hajjin bana.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne shugaban hukumar Alhazai ta Kasa Abdullahi Mohammed ya roki alhazan Najeriya da su kara hakuri da yadda jigilar alhazai zuwa gida ke yin tafiyar hawainiya.

Abdullahi ya bayyana haka ne da yake ganawa da manema labarai a garin Makka ranar Lahadi.

Ya ce zuwa kasar zai yi sauri domin an yi amfani da filayen jirgin sama biyar ne, amma a nan Fili biyu ne kawai ake amfani da su sannan ba Najeriya bace kawai za ta yi amfani da su.

Abdullahi ya yi kira ga Alhazai da su dan kara hakuri sannan su kiyaye dokar daukan kaya fiye da kilogram takwas yana mai cewa daukan kaya fiye da haka na daya daga cikin matsalolin dake hana tashi da wuri.

Ya kuma miga godiyyarsa na musamman shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakinsa Yemi Osinbajo da sakataren gwamnatin tarayya, jakadan Najeriya a kasar Saudi Isa Dodo da Mohammed Yunusa bisa kokarin da suka yi wa hukumar zuwa yanzu.

Ya kuma mika godiyarsa ga ma’akatan NAHCON da SPWB kan aiyukkan da suka yi da kuma ‘yan jarida.

Share.

game da Author