Sakatare Janar din kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) Peter Ozo-Esan ya bayyana cewa kafin nan da karshen shekarar 2018 za a fara biyan ma’aikatan kasar nan da sabuwar tsarin albashi.
Esan ya fadi haka ne ranar Talata a Abuja da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne kungiyar kwadago ta nemi gwamnati ta kara mafi karancin albashin ma’aikaci daga Naira 18,000 zuwa 56,000.
Esan ya ce kwamitin da aka kafa domin ganin hakan ya tabbata zai kammala aikin sa ne ranakun 4 da 5 ga watan Satumba.
Ya ce bayan sun kammala za a gabatar da wannan bayanai ga majalisar kasa domin su tattance tare da amincewa da kudirin ta zamo doka.
Esan ya ce da zaran wannan kudiri ya zama doka gwamnati da kamfanoni masu zaman kan su za su fara biyan ma’aikata bisa ga wannan amintaciyyar sabuwar tsari na Albashi.
A karshe Esan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su tabbatar sun yi rajista kuma sun karbi katin zaben su domin da wannan katin ne za su sami makamin koran gwamnonin da basu kulawa da su.