A doguwar tattaunawa da Gwamnan Jihar Benuwai Samuel Ortom ya yi da PREMIUM TIMES, ta bayyana dalla-dallar asalin rikicin sa da Shugaba Muhammadu Buhari da kuma rigingimun da ake samu a yankin Arewa ta tsakiya, wadanda ya ce ba rikicin makiyaya da manoma kadai ba ne ya dabaibaye yankin.
PT: Mun fahimci jirgin siyasar jihar ka ya na tangal-tangal cikin ‘yan kwanakin nan. Me ke faruwa ne?
Samuel Ortom: To, abin takaici ne kwarai, domin abin da ke faruwa a nan, da wata kasa ce mai wayewa da kuma ci gaba, to hakan ba zai faru ba. Amma nan a Najeriya, abin kamar ya ma zama kalubale a gare mu. Idan ka jajirce a kan gaskiya, adalci da bin ka’ida, to ka zama abin kalubalanta ga jama’a da yawa. Wannan shi ne abin da ke faruwa a jihar Benuwai.
Gaba dayan sabanin ya taso ne daga tsayawar da na yi ina neman kare hakkin al’ummar jiha ta. Amma ni ba ni da wata aniyar yin rigima da masu mulkin kasar nan, ko wani mutum shi daya tilo.
Ni dai na hau mulki cikin 2015, amma fadan da ake kira na makiyaya da manoma, ya dade ba tun yau ba. Daga 2011 a misali, ai ana wannan fadace-fadacen.
To mu sai muka zauna muka yi nazarin cewa, tunda dai an ce fada ne a tsakanin makiyaya da manoma, don me a kasashe kamar su Afrika ta Kudu, Switzerland da irin su Kenya duk ba a samun irin barkewar wannan rikicin? Ai a fadin duniya ana noma, kuma akwai makiyaya, amma ba a samun barkewar kashe-kashe da lalata dukiyoyi, sai nan a Najeriya.
Daga nan sai muka ga hanya mafita ita ce kamar yadda sauran kasashe suka yi, kuma suka zauna lafiya, wato a killace dabbobi kawai. Dalili kenan muka shigo da wannan doka ta hana kiwo barkatai a jihar Benuwai.
Kuma kafin a kafa dokar sai da aka kasa jihar Benuwai zuwa shiyya hudu inda aka wayar wa jama’a kai, kuma akasarin al’umma suka yi murna da wannan doka.
PT: amma duk da haka sai da Miyetti Allah ta yi kuka da wannan doka. Me ya sa?
Ortom: cewa suka yi ma ba zai yiwu a kafa wannan dokar ba. Wai su na da ‘yancin da za su rika yawon kiwo da dabbobin su inda suke ga dama, kuma ba wanda ya isa ya dakatar da su.
PT: Ashe kai ka shigo da batun dokar killace dabbobin kenan?
Ortom: E mana. Ai batun killace dabbobi wuri daya shi ne, ka tsare shabun ka wuri daya, ka tanadar musu da abincin su, har da ruwan shan su, don kada su afka cikin gonar wani ko wasu su rika yi musu barna.
PT: Ka ce rikicin ba na makiyaya da manoma kadai ba ne. Har da na me kuma?
Ortom: Kwarai kuwa, ai a kan hanyar yin wannan bayanin na ke. Mun sa wa dokar hana kiwo barkatai hannu a ranar 22 Ga Mayu, 2017, to a cikin watan Yuni, sai Miyetti Allah ta fito ta ce wannan dokar ba mai dorewa ba ce, karkon-kifi za ta yi, domin ba za su amince da ita ba. Kai har ma cewa kungiyar ta yi za ta tarkato kan mambobin ta domin su bijire wa dokar.
Ganin haka sai nan da nan na rubuta wasika zuwa Fadar Shugaban Kasa, kuma bayan na aika da wasikar sai na bi sayu da kai na domin zuwa ziyara fadar. Na rubuta wa jami’an tsaro cewa wadannan mutanen fa su na barazana. Kuma ni dama a iyar sanin da na yi musu, idan har shugabannin kungiyar Miyetti Allah ta furta wata barazana, to shikenan magana ta kare. Ni kuma sai na nemi jami’an tsaro su kama wadanda suka yi wannan barazana.
To cikin wannan shekara kuma sai wata kungiyar Fulani mai suna FUNAM ta kira taron manema labarai, ta ce za ta kaddamar mana. Ganin haka, sai na samu kwafen kalaman na su, na hada. Wasun su ma cewa suka yi ai batun na mamaye wannan yanki ne, domin wai a cewar su, yankin Benuwai din nan da muke ciki wai mallakin su ne.
PT: Ko ka samu zaunawa tare da shugaban kasa a kan wannan batun?
Ortom: Mun zauna, kuma na fada masa kukan mu, amma babu abin da aka yi, har sai cikin watan Janairu din nan, bayan mun kaddamar da dokar hana kiwo a ranar 1 Ga Nuwamba, 2017.
Wato idan ka lura mun bada rata domin kara samun maslaha, domin a cikin Mayu aka sa dokar amma ba a fara amfani da it aba, sai cikin watan Nuwamba. Muka ce matsawar makiyayi zai killace shanun sa a wuri daya, za mu zauna da shi babu wata tsangwamar juna, sai zaman lumana. Amma wanda duk ya ke ganin cewa shi ba zai iya killace shanun sa wuri daya ba, to sai ya tafi wata jihar ya nemi wani dajin da zai rika yawon kiwo da shanun sa a can.
Me zai faru, sai kawai muka wayi gari a ranar 1 Janairu, 2018, makiyaya suka kai wa jama’a mummunan farmaki, suka rika kashe jama’a har da kona kananan yara. Banda ma harbi da suka rika yi, sun kuma rika harbin jama’a da kibau, bayan sun kashe mutane kuma har daddatsa su suka rika yi.
An kawo jami’ann tsaro har da sojoji, amma kamen da aka yi bai taka kara ya karya ba. Su kuma sojoji sai ma suka rika raba takardun kiraye kirayen jama’a a zauna lafiya tsakanin makiyaya da manoma. Dalili kenan fadan a lokacin ya ki tsaywa.
Da shugaban kasa ya kawo ziyarar ta’aziyya, mun shaida masa cewa mun yi murna da kawo sojoji, amma aikin da suke yi, tamkar aikin-Baban-giwa ne. Kai, mu dai ba mu samu sauki daga kisan da mahara ke yi ba, har sai da aka kawo sojojin Operation Wild Stroke tukunna. Amma na Exercse Cat Race babu wani abin a zo a gani da suka tsinana mana.
PT: To amma ai su sojojin Operation Cat Race akwai lokacin da suka ce sun kama wani mai b aka shawara a fannin tsaro, da suka ce sun kama shi da laifin daukar nauyin masu kashe mutane.
Ortom: Ai ka ji irin ta. Maganar duk ta bata wa mutum suna ne domin a samu dalilin hukunta shi kawai. Ni dai babu ruwa na da daukar nauyin wasu kartin kauye masu kashe mutane. Kowa ya san ni, kuma duk jihar nan an san ni ko wane ne.
Saboda ma farkon abin da na fara yi da na hau mulki shi ne raba makamai daga hannun masu tayar da husuma a cikin 2015.
Har sharri ma sai da kala min wai ina daukar nauyin wasu makasa mutane su 600, kowane kuma ya na da bindiga samfurin AK47.
PT: Batun Tishaku
Ortom: Ina zuwa a kan sa dama. Ba ni na dauke shi aiki ba. Na tarad da shi ne gwamnatin da na gada ce ta dauke shi aiki a karkashin gwamnatin jihar Benuwai. Kuma tsohon Sufeto Janar na ‘Yan sandan Najeriya ne ya kawo shi domin ya rika shiga tsakanin makiyaya da kuma ‘yan asalin jiha don kada kashe-kashe su rika barkewa. An ce tubabben dan Boko Haram ne. kuma ba shi kadai ba ne na gada daga waccan gwamnatin, akwai matasa masu irin wannan aiki na Tishaku.
Ko lokacin da Buhari ya kawo ziyara, ai sai da Tishaku ya mike a gaban shugaban kasa din ya zayyana masa yadda aka yi ya zama dan Boko Haram, amma daga baya ya tuba. Ya ce masa mai bada shawara ga shugaba kan tsaro ne ma ya ceto shi lokacin da aka nemi kulla masa wani sharri. Ya kuma fada wa Buhari dai cewa Mataimakin Fufeto Janar na ‘Yan sanda da kan aiki ne a yanzu ya turo shi jihar Benuwai. An kwao kafin na zama gwamna fa.
Don haka ashe ma kowa ya san shi kenan a kasar nan, tun ma kafin na hau mulkin jihar Benuwai.
PT: Ba za mu manta ba, akwai lokacin da fadar shugaban kasa ta ce dokar da ka sa ce ta harzuka kashe-kashen da ya faru a jihar Bneuwai.
Ortom: To, idan har ka ji ministan harkokin cikin gida na irin wannan kalamin, idan kuma ka ji ministan tsaro na irin wannan kalamin dai, ko babban hafsan sojojin kasa, to wannan ya ishe ka hujjar sanin dalilin da ya sa na ke a cikin tsaka-mai-wuya.
Amma bari na tambaye ka, idan har an ce dokar da aka kafa ce dalilin kashe-kashen jihar Benuwai, to jihar Zamfara da Filato da Kaduna fa? Maganar dai ita ce waccan kungiyar Fulani da ta yi kasassabar kin bin doka, kai, ta ce ba ma magabar killace dabbobi ba ce, maganar mamaye yankin ce kawai. Zancen gaskiya kenan.