Kwamitin Hadin Guiwa na Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya dake kula da harkokin zabe ya amince a bai wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, naira biliyan 143 daga cikin kudade naira biliyan 189.2 da ta nemi a ba ta domin gudanar da zaben 2019.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya mika wannan bukata ta INEC ga Majalisa a cikin watan Yuli.
An shafe makonni da yawa ana tattauna batun wadannan kudade a zauren kwamitin majalisar.
A cikin wasikar da Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa, ya ce za a bai wa INEC naira biliyan 189.2 domin gudanar da zaben 2019, amma a fara bai wa hukumar naira biliyan 143.5 a cikin wannan shekara, sauran naira biliyan 45.6 kuma a 2019.
Sai dai kuma shi Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya nemi a ba su kudaden a lokaci daya.
Yau Litinin kwamitin ya bayyana cewa za a bai wa INEC naira biliyan 143 tukunna, bayan sun kammala wani taro da ya shafe kusan minti 40 ana tattaunawa a kai.
Sun ce sun amince da matakan da shugaban kasa ya rattaba cewa a fara bayar da naira biliyan 143 tukunna a wannan shekara.
“Mun kuma shirya karbar shugabannin INEC gobe Talata da misalin karfe daya na rana. Za mu saurari bayanan da za su mika a gaban kwamitin domin daukar mataki na gaba.
Sai dai kuma bai ce ga ranar da za a sake rattaba amincewa a ba su cikon naira bilyan 45.6 da suka rage ba.
A baya dai shugaban hukumar zaben ya bayyana dalilan da suka sa kasafin na zaben 2019 ya kai har sama da naira biliyan 180.
Mahmood ya bayyana cewa a dalilin karin yawan sabbin masu zabe, karin rumfunan zabe da mazabu da kuma karin yawan jam’iyyu duk suna daga cikin dalilan da yasa hukumar zabe ke bukatar karin kudi fiye da wanda a ka kasafta mata a kasafin kudin kasa.