Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da kungiyar likitocin Najeriya (NMA) sun hada kawance domin kula da mutanen da ke bukatar taimakon gaggawa.
Jam’in yada labarai na hukumar NEMA Sani Datti ya sanar da haka ranar Lahadi Abuja inda ya kara da cewa sun kafa wata kungiya da ake kira ‘Bilateral Technical Working Group (BTWG)’ domin tsara hanyoyin da za su iya taimaka wa wajen kula da mutane yadda ya kamata.
Datti yace shugaban hukumar Mustapha Maihaja ne ya gabatar wa shugaban kungiyar NMA da wannan shiri tasu ranar Asabar a Abuja.
” Duk da cewa muna da namu likitocin a hukumar amma hada wannan kawance da NMA zai taimaka wajen inganta kula da kiwon lafiyar mutanen da suka sami kan su cikin yanayi na neman agajin gaggawa.
” Sannan hakan zai ba mu damar fadada kwarewar mu a aikin samar da agajin gaggawa da muke yi.”