Kwanaki biyu bayan kafa dokar ta baci, matasa sun kai hari a unguwar Malali, Kaduna

0

Da yammacin Lahadi ne mutanen unguwan Malali, suka gamu da fushin wasu matasa da dauke da makamai inda suka far wa mutanen unguwar da sare-sare.

Mutanen unguwar da suka tattauna da wakilin PREMIUM TIMES sun fadi cewa matasan sun shigo unguwar daukar fansa daya daga cikin dan uwan su da aka kashe a rikicin Unguwar Yero da Kwaru ne.

Umma Dauda ta sanar wa PREMIUM TIMES cewa sun dan shiga cikin tashin hankali, kafin zuwan jami’an tsaro.

” Jami’an tsaro ne suka kawo mana dauki domin kuwa matasan da muke ganin sun shigo unguwar don daukan fansa ne suna dauke ne da zaratan makamai a hannun su.

Wani mazaunin unguwar ya furta cewa ya ga wasu mutane biyu kwance cikin jini a lokacin da ake guje-guje.

Duk da cewa mun nemi ji daga bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Kaduna hakan a ci tura, sai dai wani shugaban ‘Yan banga da ke zaune a unguwar ya shaida wa wakilin mu cewa yanzu komai ya lafa, har ma yana ganin an dan yi kame a unguwan.

Share.

game da Author