Babban Hafsan Sojojin Saman Najeriya, Sadique Abubakar, ya roki kamfanin kera jiragen yaki na Amurka da ya gaggauta turo jiragen yakin nan da ta saya samfurin A-29 Super Tucano, domin yaki da Boko Haram.
Abubakar ya yi wannan roko ne ga Taco Gilbert, mataimakin shugaban kamfanin kera jiragen a ziyarar da ya kai masa a Abuja.
Abubakar ya nuna jin dadin yadda gwamnatin Amurka ke goyon bayan yaki da Boko Haram da har aka sa hannun kwangilar saida jiragen yakin ga Najeriya.
Sai dai kuma ya ce babban abin damuwa kuma shi ne tsawon lokacin da za a shigo da jiragen a Najeriya, inji shi, za a dauki lokaci, wanda hakan abin damuwa ne matuka.
Ya fahimci cewa jirgin yakin mai cin dogon zango, ya na da jimirin lodin zabarin makamai tare da kai hari a rana da kuma dare a cikin abokan gaba.
Daga nan sai ya roki kamfanin da su gaggauta kammala kera jirgin yakin, kuma su kawo ko da guda biyu ne a Najeriya cikin wannan lokacin domin samun karin kuzarin yaki da Boko Haram.
Shi kuma Gilbert ya sha alwashin kawo jiragen domin su yi amfanin da ake so a yi da su.
Ya kuma nuna aniyar kamfanin na bayar da horo ga sojojin saman da za su rika sarrafa jiragen yakin su na kai hari da su.
Kakakin Sojojin Saman Najeriya ya bayyana cewa an gabatar wa Najeriya da mutum-mutumin jirgin samfurin Tucano ga Babban Hafsan Sojojin Sama na Najeriya.
Cikin watan Fabrairu ne Najeriya ta biya tsabar kudi har dala milyan 496 domin sayo jiragen yaki 12 daga Amurka, amma sai cikin 2020 ne za a fara kawo su.
Za a kawo jiragen tare da bama-bamai 11, da roket da kuma na’urorin sanso, masu gano lungun da mahara suka labe.
Discussion about this post