Gwamnatocin Barno da Katsina sun aikawa Alhazan jihohin su goron Sallah a Makkah

0

Gwamman jihar Barno Kashim Shettima, mataimakin sa Usman Durkwa da matar sa sun aika wa Alhazan jihar Barno naira 45,000 kowannen su a matsayin goron Sallah.

Gwamna Shetima ya ba alhazan naira 30,000, mataimakin gwamna ya aika da naira 10,000, ita kuma matar mataimakin gwamna ta ba kowannen su naira 5,000.

Kakakin hukumar Alhazai ta Jihar Aishatu Ibrahim, ta sanar wa alhazan haka a lokacin da take mika musu sakon gwamnatin a Makka.

Alhazan sun yi wa gwamnatin jihar Addu’oi da yi mata fatan alkhairi.

Haka ita ma jihar Katsina ta raba wa Alhazan ta goron Sallah na Riyal 300 ga kowannen su a Makka.

Babban Darektan hukumar Alhazai na jihar Muhammad Rimi, ya bayyana wa alhazan Katsina a garin Makka.

Yace gwamna Masari ne ya ce a basu wadannan kudade goron Sallah.

Share.

game da Author