Majalisar Koli ta Musulunci, NSCIA, ta maida wa Bishop Mathew Hassan Kukah martani cewa, an fi nuna wa Musulmai bambanci da wariya a kasar nan, fiye da zargin sa cewa an fi yi wa Kiristoci.
Makonni biyu da suka gabata ne, a wani taron kaddamar da littafai da PREMIUM TIMES ta shirya a Abuja, Kukah ya bayyana cewa ana nuna wa kiristocin kasar nan bangaranci, musamman a Arewa inda a wasu manyan makarantu ba a yarda a gina coci-coci don dalibai kiristoci ba.
Kukah ya kafa misali da Jami’ar Bayero ta Kano da kuma Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato.
Sai dai kuma a cikin martanin da Majalisar Kolin Harkokin Musuluncin Najeriya ta maida masa, Jami’in Hulda da Jama’a Aselemi Ibrahim ya ce dama can Kukah ya yi kaurin suna wajen ruruta siyasar addini da kuma yayata karairayi a kasar nan.
Jami’in ya buga misali da yadda aka rika kai ruwa rana dangane da batun sa hijabi a makarantu da sauran kuntatawa da ake yi musulmi da dama.
“In banda neman haddasa husuma da tashin-tashina, ai bai kamata ma ya yi wannan magana ba. Tsakanin babbar Sakateriyar sa ta Darikar Roman Katolica da Fadar Sarkin Musulmi, ai bai fi tazarar tafiyar minti uku ba.
“Lokacin da aka bude fadar Katolika ta Sakkwato, duk da cewa gwamnan jihar musulmi ne, amma sai da ya halarta.
Sarkin Musulmi ba ya kasar aka bude ta, amma sai da ya tura tawaga ta musamman ta wakilce shi.”
Daga nan sai kungiyar ta ci gaba da lissafa bambanci, wariya da kuntatawar da musulmi suka fuskata ko suke fuskanta har yanzu.
“Shi fa Kukah din nan ya kau da ido daga irin dama da ‘yancin da ya samu a Arewa har ya ke jagorantan kantama-kantaman coci-coci na biliyoyin nairori. Amma abin mamaki, ya manta ko kuma ya kauda kai daga irin kuntatawar da Kiristoci Gwamnoni ke wa musulmai a kudancin kasar nan, tare da tauye musu ‘yanci.
Daga nan ya ci gaba da nuna yadda ake maida addinin musulunci saniyar-ware a kudancin kasar nan.
“A kudancin kasar nan fa kungiyar kiristoci ta CAN, kiri-kiri ta ke nuna goyon baya har suka rubuta takardun goyon bayan wani gwamna a lokacin zabe. Amma idan wata kungiyar musulmi za ta yi haka, to shikenan ta bani ta lalace a hannun kiristocin kasar nan.”
“A fili gwamnonin kudancin kasar nan ke daukar nauyin shirye-shiryen kiristoci na miliyoyin nairori a gidajen talbijin, amma abu kadan za a yi a Arewa idan wani gwamna ya dauki nauyin wasu tsirarun musulmi zuwa aikin Hajji, shikenan sai kiristoci su kama kakabi da hayagaga.
“Munaficci ya yi wa Kukah katutu, domin ya na sane da halin da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Rivers ke ciki, inda darikun kiristoci har shida kowace da kantama-kantaman coci-coci sun gina ko kuma an gina musu a cikin jami’ar. Amma hukumar makarantar ta ki yarda a gida masallaci a cikin jami’ar.
“Dan wurin da dalibai musulmai na jami’ar suka share wuri suka kafa ‘yar rumfa su na Sallah, rushe wurin aka yi, aka kwace musu kayan tun a ranar 25 Ga Janairu, 2012.
Kungiyar Musulmai ta ce an kai kara a Babbar Kotun Tarayya ta Fatakawal, aka sahale musu dama a ranar 19 Ga Fabrairu, 2013.
“Maimakon jami’ar ta dubi zumuncin zaman tare tsakanin juna, ta bada damar gina masallaci kamar yadda kotu ta bayar, sai aka daukaka kara, abu dai har a kotun koli.”
“Dubi irin mashahuran dattawa musulmi da muke da su a kudancin kasar nan. Amma har sai da wata kungiyar Musulmi ta Yankin-kudu maso kudu ta yi nuni da irin rashin adalcin da kungiyar Afenifere ta ke nunawa, wajen kin daukar manyan musulmai Yarabawa cikin kungiyar Dattatan Yarbawa zalla ta Afenifere.
Daga nan sai ta tunatar da Kukah yadda marigayi Bola Ige ya rika nuna wa musulmin jihar Oyo kiyayya a sarari kafin mutuwar sa.
“Ai ganin yadda Gidan Talbijin na Channels bai yarda ya yayata sha’anin addinin Musulunci, ko da kuwa za a biya, amma ba su yarda su gudanar da shirye-shiryen da kungiyar mu da nema a rika yi mu na biya. Wannan duk ba wani abu ba ne a wajen Mathew Hassan Kukah. Amma lokacin da jaridar Concord ta Marigayi MKO Abiola ta ce ba za ta tallata giya ba, aka yi masa ca sannan aka dangantashi da mai tsatssaurar ra’ayi.