Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu da ke Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, ta umarci Shugaban Sojojin Najeriya, Tukur Buratai ya biya diyyar naira miliyan 11 ga wasu ‘yan jihar Gombe 11 da ya ce an tsare ba da hakkin komai ba.
Ojukwu ta ce tsare su da aka yi tun daga ranar 6 Ga Yuli, da aka tsare su, an yi hakan a bisa karya dokar Najeriya, don haka tsare su da aka yi haramtacce ne.
Wadanda sojojin suka tsare, sun hada da James Yusuf, Ishaya Ali Poshiya, Nehemiah Yohanna Poshiya, Husseini Poshiya, Hamma Poshiya, Yusuf Mafindi, Yila Boyi, James Bare, Ezekiel Dandaudu, Ali Ishaku da kuma Ilya Bala.
Ojukwu ta ci gaba da zartas da cewa Buratai zai biya diyyar naira milyan 1 ga kowane wanda aka tsare di su sha daya.
Ta ci gaba da yin gargadin cewa haramun ne jami’an tsaro su ci gaba da tsare mutum sama da lokuta ko kwanakin da shari’a ta amince a tsare shi.
Takardar karar da ke gaban alkali ta nuna cewa an tsare su bisa zargin kisan wani mai suna David Jauro Stephen.
Takardar kara ta nuna cewa an kashe Stephen a gonar sa, kuma an zargi wasu mutanen kauyen Shangom.