IPOB: Kotu ta saki mata 100 da aka tsare

0

Kotun majestare dake garin Oweri jihar Imo ta yanke hukun sakin wasu mata 100 da aka tsare a dalilin zanga-zanga da suka gudanar suna kora ga gwamnati da ta saki shugaban kungiyar ‘yan tsagra masu neman a raba kasa Najeriya.

An tsare matan ne ranar 18 ga watan Agusta a daidai suna yin zanga-zangar.

Lauyan dake kare wadanda aka tsare, Sam Amadi ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa tabbas an sake matan sannan an yi watsi da shari’a kwata-kwata.

Dama can tun bayan tsare wadannan mata kungiyoyin rajin kare hakkin dan adam daban-daban suka fito suka kyamaci tsare wadannan mata.

Idan ba a manta ba, Nnamdi Kanu ya ha bace ne bat tun bayan arangama da ‘yan kungiyar IPOB suka yi da dakarun sojin Najeriya. Har yanzu dai babu labarin sa.

Share.

game da Author