Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da saka dokar hana walwala a Unguwar Yero da Kwaru Badarawa dakr garin Kaduna a dalilin rikici da ya barke a tsakanin matasan Unguwannin.
Wannan rikici yayi sanadiyyar rasuwar wasu mutane biyu.
Gwamnan jihar Nasir El-Rufai da mataimakin sa Barnabas Bantex sun kai ziyarar jaje ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su a rikicin.
El-Rufai ya ce gwamnati ba za ta zuba ido ta bari wasu bata gari na yin abin da suka ga dama a jihar ba, sannan gwamnati ta ce daga yau an saka dokar hana walwalan jama’a a wadannan unguwanni daga karfe 7 na yamma zuwa 7 na safe.
Bayan haka ya roki mazauna wadannan unguwanni da su zauna lafiya da juna sannan su guji shigo da kabilanci ko addini a zamantakewar dake tsakanin su.
Wasu mazauna unguwannin sun roki gwamnati da ta sa ido ga ayyukan matasa ‘yan ta’adda a musamman wadannan unguwanni.

” Shaye-shayen kwayoyi ne ke tada wadannan fitintinu. Duk a lokaci irin na sallah ko makamancin haka sai kaga an sami irin wadannan hare-hare kuma duk ya na faruwa ne daga wajen aikata irin wadannan shaye-shaye ne.” Inji Baban Amir da wasu mazauna unguwannin.
Discussion about this post