Rufa-rufa da harkallar Ministan Shari’a, Malami

0

Kalaman da Ministan Shari’a, kuma Antoni Janar na Najeriya, Abubakar Malami ya yi dangane da bijire wa umarnin kotu da Gwamnatin Tarayya ta yi wajen kin sakin Sambo Dasuki, kamar yadda kotu ta bada umarni, ya janyo masa caccaka da ragargaza daga wasu manyan lauyoyin kasar nan.

Abin ya kai har wasu na kiraye-kirayen a cire masa alkyabbar kima da martabar aikin lauyan da ya ke takama da ita.

Lauyoyin dai sun nuna cewa kin bin umarnin kotu da gwamnatin tarayya ta yi, hakan ba bakon abu ba ne ga gwamnatin Muhammadu Buhari.

Matsayin da Malami ke kai, na goyon bayan ci gaba da tsare Sambo Dasuki, ba shi kadai ba ne hanyar da Malami ya bi wajen karya doka ta hanyar kin bin umarnin kotu, a matsayin sa na babban jami’in shari’a na farko a yau a Najeriya.

MALAMI: KOWA YA YI RAWA A KASUWA, BA YAU YA FARA BA

Rufa-rufar da Abubakar Malami ya tsoma kafar sa tsamo-tsamo wajen dawo da Abdulrashid Maina da sake maida shi kan aikin gwamnatin tarayya abu ne da ya dora alamomin tambaya a kan alkiblar Malami.

Idan aka ci gaba da lissafi, akwai rawar da ya taka wajen neman a biya wasu lauyoyi lada ta zunzurutun kudi har dala miliyan 17, saboda rawar da ya ce sun taka wajen maido da tsabar kudaden da Abacha ya wawure zuwa kasashen waje.

An yi mamakin yadda Malami ya shige gaba ya nemi a biya su kudin alhali an shigar da su maganar a lokacin da an kusa biyan kudin, wannan ma wani abin dora masa alamomin tambaya ce a kan kumbiya-kumbiyar sa.

Sai kuma wani tuggun da gadar-zare da aka yi zargin ya shirya wajen bai wa Gwamnatin Tarayya shawarar daina bincike da bibiyar harkallar dala bilyan 1.1 ta harkallar rijiyar mai ta Malabu Oil.

WANE NE MALAMI?:

Kafin zaman sa Ministan Shari’a kuma Antoni Janar, Abubakar Malami shi ne mashawarcin jam’iyyar CPC a kan al’amurran shari’a, kuma lauyan jam’iyyar, wadda Buhari ya kafa bayan ficewar sa daga ANPP a cikin 2010.

Bayan nada shi ministan shari’a, an yi tsammanin Malami zai rika bin doka da oda da kuma umarnin kotu sau da kafa. Sai dai ashe ba haka ba.

Farkon dawowar mulkin dimokradiyya a cikin 1999, sai gwamnatin tarayya a karkashin mulkin shugaban kasa na lokacin, Olusegun Obasanjo ta yunkura domin ganin an dawo da dala milyan 321 da tsohon shugaba na mulkin soja, Sani Abacha ya wawura.

Daga nan sai gwamnati ta dauki hayar wani lauya mai suna Enrico Monfrini, domin ya bi sawun yadda za a maido kudaden a nan gida Najeriya.

Bayan sama da shekaru goma ana tirka-tirka, sai kamfanin Monfirini ya kammala wani bangare na kudaden daga wasu bankuna da ke kasar Luxemburg.

An kammala wannan yarjejeniyar ce a cikin 2014 tare da Ministan Shari’ar kasar Switzerland, aka sa hannun yarjejeniya tsakanin kasar da Najeriya cewa za a yi amfani da kudaden a Najeriya ta hanyar da ta dace.

Shi kuma lauya aka biya shi ladar aikin da ya yi.

An kammala wannan yarjejeniyar biyan lauya a lokacin Malami.

Babu wani abin da ya rage sai sa hannu tsakanin gwamnati da gwamnati domin a maido kudin.

Kwatsam a lokacin da Malami ya zama ministan shari’a, a cikin 2015, sai ya sake daukar wasu lauyoyi daban har su biyu a bisa wai su yi aikin dawo da kudaden Najeriya – aikin da lauya Monfrini ya yi shekarun baya aka biya shi kudin sa.

Kirikiri Malami ya murje idanu ya ce a biya wadannan lauyoyin rana-tsaka har dala miyan 16.9, kudin da sun haura wadanda aka bai wa lauya Monfrini nesa ba kusa ba.

ABOKIN DAMO GUZA

An gano cewa lauyoyi biyu, wato Oladipo Okpeseyi da Temitope Adebayo da Abubakar Malami ya dauka aikin dawo da kudaden da tuni wancan lauya na farko ya yi, ashe abokan aikin Malami ne a lokacin da ya ke lauyan jam’iyyar CPC.

Yayin da Abubakar Malami ya ga tusa ta kare wa bodari, sai ya ce ai ya dauko hayar lauyoyin da ya ce ya dauko, saboda Momfrini ya nemi a ba shi karin kashi 20 bisa 100 na jimlar kudaden.

Sai dai kuma kamfanin Monfrini ya karyata Malami, ya ce karya ya ke yi masa.

“Ban taba neman wadannan mahaukatan kudaden da Malami ya yi min kazafin wai na nema har kashi 20 bisa 100 na milyoyin kudaden.” Haka Monfrini ya maida wa Malami martani.

MANUNIYA

Harkallar dawo da kudaden da Abacha ya wawura da Abubakar Malami ya jefa kan sa, ba ita kadai ba ce kamar yadda tun da farko aka lissafa wasu a farkon wannan nazari kan Ministan Shari’a Malami.

Sai dai kuma ya na da kyau a karkare da asarkalar boye shari’a da ya ke da shi a shari’ar wani dan sanda da ya tafka kisan kai ba. Wannan kuma rikicin shari’a ne na wasu mutane shida da jami’an tsaro suka kashe su shida a Apo, Abuja, inda aka kashe wasu ‘yan tireda shida, wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.

An ce an harbe su ne jim kadan yan sun yi tankiya da wani dan sanda mai mukamin mataimakin kwamishina a wani gidan shakatawa, da ke kan titin Gimbiya, cikin Area 11, Abuja.

Share.

game da Author