Babban hafasan sojin Najeriya Janar Tukur Buratai ya shaida wa sojojin Najeriya da suka sami rauni a yaki da Boko Haram cewa sadaukar da jikin da rayukan su da suka yi ba zai tafi a banza ba.
Buratai ya fadi haka ne da ya ziyarci wasu daga cikin sojojin da aka ji wa rauni a filin daga da a ka kwantar da su a asibitin dake samun kula a asibitin (DMSH)’ dake garin Maiduguri.
Bayan yi musu addu’ar Allah ya basu lafiya, ya ce za a wadata su da duk maganin da suke bukata domin samun lafiya cikin gaggawa.
Shugaban asibitin Samuel Adama ya jinjinawa Buratai kan wannan ziyara da yayi wa sojojin da ke kwance a asibitin.
Sannan kuma da yin amfani da wannan dama don yi musu barka da Sallah.