Buhari Ne Alƙiblar Siyasa Ta, Amma Siyasar Sa Ba zata Makantar Dani Ba – Aminu Arzika

0

Sanin kowane cewa ni Siyasa ta ilahirinta Shugaba Muhammadu Buhari ne alƙiblarta tun ina ƙaramin yaron da baisan abunda ake kira da siyasa ba har nagirma cikin wannan soyayyar kuma har yau har gobe ina bisa wannan turba Insha Allah sai dai Son danake yiwa Buharin bazai makantar dani ba har in fara siyasar muguwar adawa da wani ko ɓatanci ko ƙazafi DSS.

A gaskiya ina son Buhari ne saboda nayi imani cewa shi kaɗaine cikin shuwagabanni da yakeda manufa ta ƙwarai ga wannan ƙasar tamu kuma abin ƙaunarmu, wanda hakan yasa nasha alwashin duk wanda zai bada goyon baya ga wannan tafiyar ta Shugaba Muhammadu Buhari to nikuma zan goyi bayan tafiyarshi kuma ko waye naga cewa yana son kawo cikas ga wannan tafiya to munyi hannun riga dashi.

A gaskiyar magana nayi siyasar gwamnan jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal sosai kuma na bada gudunmuwa gwargwadon halina domin inga cewa ya ɗare siyasar gwamnan Sokoto, kuma ansamu nasarar haka sannan nashiga cikin miliyoyin mutanen da suka tayashi murna saidai duk da haka a shirye nake da infita daga tafiyarshi a duk lokacin da nagane cewar baya cikin waɗanda ke goyon bayan fafutukar gyaran ƙasarnan ma’ana baya cikin tafiyar Muhammadu Buhari.

Koda yake yanzu haka bayada matsayar jam’iya, kamar yanda yayi bayani a hirarshi da BBC to wallahi nima haka nake banida wata matsaya akan tafiyar shi, sai dai koda banbi tafiyarshi ba Allah yasan bazanyi siyasar adawa dashi ba, sannan bazan shiga wani sha’ani na ɓatanci ko ƙazafi gareshi ba, sai dai kowa ya kama gabansa. Kuma ina roƙon masuyi dasu san cewa shi Allah idan baka ganinsa to shi yana ganinka kuma yafi kusa dakai bisaga jijiyar dake ɗauke da wuyanka, da fatar zasu dubi wannan suji tsoron Allah su daina.

Duk da haka idan naji wani tonon silili akan gwamnati bazanƙi neman ƙarin haske ba domin a fitardani daga duhu kada in zauna tunanin abunda bashine dai-dai ba kuma insha Allah idan al’umma na buƙatar wani aiki mai amfani to zanyi amfani da muryata domin neman ayi wannan aikin saboda gwamnati ta al’umma ce kuma domin al’umma kuma bugu da ƙari kundin tsarin mulki ya bani damar hakan.

Babban gurina shine inga cewa ansamu haɗin kai da cikaken zaman lafiya a ƙasarnan, babu wani tashin hankali babu husuma babu kisisina babu munaficci.

Da fatar Allah yasa mudace ya ganar damu gaskiya.

Share.

game da Author