Matasan Arewa suna da Arha a Fagen Siyasa, Daga Mustapha Soron dinki

0

Matasan Arewa a bangaren siyasa sun bambanta da na Kudu.Idan muka kalli yadda matasanmu suke rayuwa a duniyar siyasa zamu tausaya musu saboda basu da tsada wajen sarrafawa.A Arewacin Najeriya ne zaka samu saurayi yana yawo da barandami da gora yana kare ‘yan siyasa ba tare da yaci lafiyayyen abinci ba a ranar.Sannan a Arewa ne zaka samu saurayi ya kai shekara goma yana bin ‘yan siyasa ba tare da yaci ribar dubu goma ko aikin da za’a bashi dubu goma ko su yi tunanin mayar dashi makaranta. Muna kallo,a Arewa ne zaka samu matasa a filin zabe suna siyar da kuri’arsu ana basu naira dari biyar da sunan ‘tsari’.

Kowa ya sani a Arewa ne zaka samu matasa suna saran junansu akan ‘yan siyasa a yayin da babu shinkafa kwano biyar a gidajensu.Babu shakka a yankinmu ne zaka samu makauniyar soyayyar dan siyasa shiyasa muka zama kamar kwallo a cikin filin wasa kowa bugamu yakeyi.

Mustapha Soron Dinki

Mustapha Soron Dinki

Matasan mu ne kawai zaka samu a cikin igiyar zato, basa cigaba amma kullum suna cikin jiran tsammani.Sai ka samu mutum tun yana shekara ashirin yake jagaliya har ya kai shekara talatin da biyu yana yi. Kaga dai an cinye zango uku yana waje daya.

Nasan za’ayi mamaki idan nace,duk maganar talauci da jahilci da ake alaqantamu dasu sun samo asali ne daga yadda muka samu kanmu a duniyar siyasa.Ko dai wanda bai yi karatu ba yasan siyasa da ilimi ba’a rabasu,a tsarin gwaunati babu tsari mai aiki da ilimi da kuma bawa samar da ilimi karfi kamar siyasa saboda sai da ilimi ake cigaba.Gwaunan Kano, Dr Ganduje yace “cigaba bai taba samuwa ga mutane marasa ilimi ba a duniya”.Wannan maganar tana cikin littafinsa mai suna “Democracy and local government administration in Nigeria”.

Abun tambaya a nan shine,shin matasan Arewa basa neman ilimi ne? Gaskiya suna yi tunda ko a makon da ya wuce an samu wani Bakatsine mai suna Bashir Dodo ya cinye gasar masana laurar idanu da akayi a Portugal.Ga kuma mutane irinsu Aliyu Jelani da sauransu.

Amma gaskiya abunda ya shafi siyasa basa amfani da iliminmu wajen neman makomar rayuwarsu.

Tsakani da Allah haka makotanmu matasa ‘yan kudu suke? Kada mu saka son zuciya,mu duba mu gani.Ba zaka ta6a ganinsu suna jagaliya ba irin wannan ta sara suka sannan basa yin makauniyar soyayya.Duk inda ka gansu,to kafin su yi za6e sai an qulla yarjejeniya dasu da ‘yan siyasa.Sannan suna da wayewa wajen kafa kungiyoyi kamar yadda doka ta basu dama.Nayi mamaki watarana a kudu da naga wata karamar kungiya ta gayyato gwauna saboda wasu matsalolin al’umma.

Amma mu a Arewa bama amfani da baiwarmu,na farko dai muna da yawa,na biyu muna da karatu na addini da na boko.Shi fa ilimi sai anyi aiki dashi yake zama mai amfani sannan kuma sai mun yi hakuri mun bi doka.

Allah yasa mu ga alheri

Share.

game da Author