Sarkin Daura Umar Faruq, ya nada tsohon gwamnan jihar Abia Orji Kalu sarautan Danbaiwan-Hausa ganin irin gudunmawar da ya bada wajen ci gaban jihar sa da kasa baki daya.
Sarki Faruq ya bayyana cewa wannan sarauta da aka yi wa Kalu zai zama kamar jakadan Hausa a yankin kasar Igbo.
” Wannan sarauta a kasar Daura ce kawai za a iya baka ita. Kuma mun yi haka ne ganin irin goyon baya da kauna da kake nuna wa dan mu, shugaba Muhammadu Buhari.
” Muna rokon ka da ka ci gaba da wannan zumunci da ka kulla da mu.
Kalu ya gode wa masarautar Daura da irin wannan karramawa da ta yi masa, sannan daga bisani ya garzaya zuwa gidan shugaba Muhammadu Buhari domin isar da gaisuwar sa.
