‘Yan Ta’addan da aka fatattaka daga Zamfara na shigo mana Katsina – Gwamna Masari

0

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya yi kira ga mutanen jihar Katsina da su tona asirin duk wani bako da ya garzayo kauyukan jihar da basu amince da shi ba.

Masari ya bayyana haka ne a ziyarar sallah da sarkin Katsina Abdulmumini Kabir ya kai masa a fadar gwamnati.

Masari ya kara da cewa da yawa cikin mahara da ‘yan ta’adda da aka fatattaka daga dazukan jihar Zamfara suna yada zango a dajin Rugu dake jihar.

” Ina rokon ku da ku tona asirin duk wani bako da baku amince da shi ba. Domin babu wani amfani da za su kawo mana jiha sai dai tashin hankali.

Bayan haka Masari ya roki mutanen jihar da su tabbata sun mallaki katin zabe.

Da yake nashi bayanin, Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir, ya roki mutanen jihar musamman matasa da su guje wa shan miyagun kwayoyi sannan su zamanto masu kula da lafiyan su da tsaftace muhallan su.

Abdulmumini-Kabir-Usman

Abdulmumini-Kabir-Usman

Share.

game da Author