Buhari zai lashe zaben 2019 cikin sauki – Lai Mohammed

0

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su guje wa zaben wadanda za su dawo kan mulki a kasar nan domin su wawure dan abin da ya rage ba su wawura a baya ba.

Lai yayi wannan kira ne a ranar Sallah, a cikin sakon jawabin da ya yi wa jama’a a garin sa na haihuwa, Oro da ke kusa da Ilorin, jihar Kwara.

“Shekarar 2019 ita ce shekarar ‘yan Najeriya za su zabar wa kan su mafita.

“Shekara ce da ‘yan Najeriya za su zabar wa kan su ko dai su ci gaba da bin tafarkin ci gaban kasa da wannan mulki ya dauko a kan turba, tun 2015, ko kuma su sake rumgumo wa kan su alakakai da jangwangwamar da ta dukunkune kasar nan ta hanyar wawure dukiya da rashin samar da ci gaban kasa.” Inji Lai.

Ya kara da cewa ya zama wajibi ‘yan Najeriya su jajirce kada su bari wasu su sake lababowa su warware tubkar igiyar da wannan gwamnati ta daure tattalin arziki, ta hana shi komawa baya ba.

Daga nan ya gode wa ‘yan Najeriya dangane da goyon bayan da suke bai wa wannan gwamnatin gami da jajircewa da kuma dauriya. Sai ya ce wannan gagarimar sadaukarwa da suke yi, ba za ta tafi a banza ba.

Lai ya ce ya tabbatar cewa ganin irin goyon bayan da ake nuna wa Buhari a kasar nan, to zaben 2019 zai zama tamkar wasan yara a wajen Buhari da kuma jam’iyya mai mulki, APC.

Ya yi nuni da cewa Buhari ba zai hadu da wata adawa ko kalubale a zaben 2019 ba, zaben zai zame masa tamkar shan koko wajen sauki.

“Ni dai na tabbatar da cewa a yadda ‘yan Najeriya suka yi nasarar tsallake tekun maliya, ba za su yarda su koma kasar Masar ba.”

Daga nan sai Lai ya yi ta bada labara daki-daki, na irin dimbin nasarorin da ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta samar a kasar nan daga 2015 zuwa yau.

Share.

game da Author