Sarki Shehu ya gargadi matasa da su guji shaye-shayen miyagun kwayoyi

0

A yau ne babban limamin masallacin Idi dake rukunin gidaje masu saukin kudi wato Low-Cost dake Kofar Gayan, Zaria Muhammed Aliyu ya yi kira ga mutane da su guji zaman kashe wando, su nemi aikin yi.

Aliyu ya fadi haka ne da yake karanta khudubar sa na ranar Idi.

Ya ce aikin yi na taimaka wa mutum wajen samun abin dogaro ga, musamman ga masu iyali.

Ya ce addinin musulunci ya kyamaci mutum rago sannan ya kara da cewa isan ka duba kayi nazari duk annabawan Allah basu yi zama haka kawai ba.

“Ina kira a gare ku da ku koyi sana’ar hannu domin samun abin dogaro ga cewa rashin yin haka ne shaidan ke raya wa mutum a zuciya ya fara neman yin sata ko son abin wani.

Bayan an kamala sallan Idi mai martaba sarkin Zazzau Shehu Idris ya yi kira ga matasa da su nisanta kan su da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Sarki Shehu ya kuma yi kira ga iyaye da su mai da hankali wajen yi wa ‘ya’yan su tarbiyya na gari.

Share.

game da Author