Babban limamin masallacin Ijebu-Ode Mufutau Ayanbadejo ya koka kan yadda yadda cin hanci da rashawa ke kara yi wa kasa Najeriya katutu.
Ayanbadejo ya fadi haka ne a khudubar da ya karanta a masallacin idi yau Talata a garin Ijebu. Sannan ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen samar wa ‘yan Najeriya sauki a rayuwa a matsayin sa na shugaban kasa.
“Da akwai mamaki yadda masu aikata cin hanci da rashawa ke tafiyar da al’amuran su a kasar nan kamar basu aikata komai ba duk da shaidar da ake da su na aikata hakan.
“Kamata ya yi a kafa tsauraran dokoki da za su hukunta mutane masu aikata laifuka irin haka musamman wadanda ke rike da manyan mukamai a gwamnati domin sauran mutane masu yin haka su dauki darasi”.
A karshe ya yi kira ga ‘yan siyasar kasar nan da su zama masu fadin gaskiya don gujewa fushin mutanen da suke wakilta da kuma fushin Allah.