ZABEN 2019: ‘Yan Najeriya sun gudanar da addu’o’i na musamman a filin Arfa

0

A yan litinin ne, wato 9 ga watan Dhul-Hijja, kuma ranar Arfa, ‘yan Najeriya da suka tafi aikin Hajji suka gudanar da addu’o’i na musamman a filin Arfa.

Jakadan Najeriya a kasar Saudi, Mohammed Dodo da shugaban hukumar Alhazai ta kasa, Abdullahi Mohammed ne suka jagoranci dandazon Alhazan a filin Arfa.

Dodo ya ce yin irin wannan addua ya zama dole ganin cewa kafin Hajji mai zuwa an yi zaben 2019.

” Wannan shine Hajji ta karshe da za ayi kafin zaben 2019. Shine ya sa muka ga ya dace a yi irin wannnan addu’o’i domin Allah ya sa a yi zabe lafiya.

Shi kuwa shugaban hukumar Alhazai Abdullahi kira yayi da a cigaba da addu’o’i domin samun zaman lafiya a kasa Najeriya da kuma yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’o’i na musamman.

Share.

game da Author