Rundunar ‘yan sanda sun fada tarkon masu yada labaran karya kan Samuel Ogundipe – Babban Editan PREMIUM TIMES

0

Babban editan jaridar PREMIUM TIMES Musikilu Mojeed ya karyata labarin da ya karade shafunan sada zumunta da wasu shafunan jaridu a yanar gizo cewa wai an tilasta wa Samuel Ogundipe ya fadi cewa wai shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki na da hannu a badakalar labarin da ya rubuta.

Wasu kafafen yada Labarai sun ruwaito cewa wai an tilasta wa wakilin PREMIUM TIMES da rundunar ‘yan sanda suka tsare a dalilin wani labari da ya rubuta ya ambato sunan Saraki a badakalar.

An tsare Samuel Ogundipe a hedikwatar ‘yan sanda dake Abuja a makon da ya gabata ana tuhumar sa da ya bayyana inda ya sami bayanan wani labari da ya rubuta aka wallafa a jaridar.

Bayan an bada belin sa ranar Juma’ a wasu kafafen yada labarai suka rubuto labaran karya cewa wai an muzguna masa sannan an tilasta masa da ya ambaci sunan Saraki.

” A haka ne rundunar ‘yan sandan ba tare da sun yi bincike ba suka rubuta wasikar mai da martani cewa wai basu muzguna masa ba, sannan ba a tilasta shi ya ambato sunan Saraki a lokacin da yake tsare a wurin su.

” Ya kamata ace sun nuna kwarewa wajen bincikan wannan Labarai tukunna kafin su maida martani. Suma sun fada cikin masu yin amfani da labaran karya.

” Mu na so mu sanar muku cewa rundunar ‘yan sanda basu muzguna wa wakilin mu kuma basu tilasta masa ya ambaci sunan kowa ba a lokacin da yake tsare.

Mojeed ya kara da ce tun da aka tsare Ogundioe har ya fito babu tak da ya ce ma wani ko gidan jarida. Sannan Premium Times ba za ta yi wa rundunar ‘yan sandan kazafi ko karya ba cewa wai sun yi abin da ba su yi ba.

” Su dai da suka fada tarkon masu yada labarai karya, toh sune za su koma su sake duba inda suka sami wannan labari da har suke rubuta wasikar maida martani a kai.” Inji Mojeed.

Share.

game da Author