Masu taimakawa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal 252 ne suka sanar da dawowa jam’iyyar APC, cewa ba za su iya ci gaba da zama a jam’iyyar PDP ba.
Idan ba a manta ba gwamna Aminu Tambuwal ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP tare da wasu daga cikin magoya bayan sa a Sokoto.
Jagoran hadiman Tambuwal da suka komo APC daga PDP Ibrahim Haske, kuma mai magana da yawun sauran masu taimakawa Tambuwal ya ce dukkan su sun yanke wannan shawara ne ganin cewa ba za su iya aiki karkashin jam’iyyar PDP ba.

” Mu dinnan gaba dayan mu ‘yan APC ne ba zamu iya ci gaba da zama a inda ba gidan mu bane. Gaba dayan mu mun dawo APC.
Haka shima Abdullahi Sokoto da hadimin gwamna ne ya bayyana cewa yin haka da suka yi shiri ne domin tabbatar da ganin Buhari ya lashe zaben 2019.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Sokoto Sadiq Achida, ya jinjina musu sannan ya tabbatar musu da cewa jam’iyyar APC zata saka musu da dubun Alkhairi.
Discussion about this post