Osinbajo ya rattaba hannu kan sabbin dokoki uku

0

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya sanya hannu a kan kudirori uku, inda a nan take suka zama dokoki.

Ya sa wa kudirorin hannu sun zama doka ne, bayan da Majalisar Tarayya ta turo wa Ofishin Shugaban Kasa kudirorin. Osinbajo ya musu hannu a matsayin sa na Mukaddashin Shugaban Kasa.

Haka wata sanarwa daga sa hannun kakakin Osinbajo, Laolu Akane ta bayyana, inda ya ce tun a ranar Juma’a ya sa wa dokokin uku hannu.

Akande ya ce akwai dokar Hukumar Kula da Ma’aikatan Babban Birnin Tarayya, Abuja, ta 2018; akwai Dokar Kafa Cibiyar Binciken Gandun Daji ta 2018; akwai kuma Dokar Kafa Cibiyar Binciken Fasahar Magunguna ta Tarayya, ta shekarar 2018 a Jos.

Ya ce kafa hukumar kula da ma’aikatan FCTCSC, ta Abuja, dama tun cikin oka ta 303 aka amince a kafa ta.

Wannan hukuma, Shugaban Kasa ya ba ta karfin hukunta duk wani ma’aikacin gwamnati da aka samu ya da aikata ba daidai ba.

Ita kuma dokar binciken gandun dazuka, za ta bada karfi wajen bincike, wayar wa jama’a kai a kuma bayar da horo.

Wannan cibiya za ta kasance a Ibadan ne zai kasance babbar heikwata din ta.

Ita kuma cibiyar binciken fasahar magunguna a za a kafa aJos, za ta zama ta na gudanar da kwasa-kwasai na difloma da kuam horaswa da gudanar da bincike.

Share.

game da Author