‘Yan kasuwa da dillalen Raguna suna kokawa matuka kan yadda mutane ba su zuwa siyan ragon sallah.
” Mu dai a Kaduna bamu san yadda zata kaya ba domin kuwa an kawo raguna amma babu masu siya. Ni nan na kawo raguna sun kai 50 amma zuwa yanzu ban siyar da fiye da 10 ba. Bamu sani kila ko zuwa gobe da jibi a samu kasuwa ba.
Shima wani dan kasuwa dake sana’ar saida raguna a Kano ya tsokata mana cewa laillai fa akwai matsala babba a kasuwar rago na wannan shekara a jihar.
” Kila dai ko don dabbobin sun yi yawa ne a kasuwa amma kam mutane kalilan ne suke siyan ragunan. Kowa ka taba zai ce maka babu kudi ko kuma ba’ayi albashi ba.
Sai dai kuma wasu da yawa na ganin za a sayi ragunan, zuwa gobe da jibi.
” Akwai sallar da murane ba su sayi ragunan da wuri basai kamar zuwa ranar Sallah, da bayan sallah ma sannan suka sayi ragunan, kuma sun kare duka. Haka yanzu ma muna sa ran hakan zai faru.
Wani mazaunin garin Kaduna, Ahmed Mohammed Majikiran masarautar Lere da ya zanta da wakilin mu a Kaduna, ya bayyana cewa ba wai rashin kudi bane kawai matsalar da aka samu da mutane ke ganin kamar ba za a siya ragunan ba.
” A nawa ganin kuma a matsayina na shugaban al’umma, ragunan ne aka kawo su da yawan gaske. Ko ina kabi zaka ga rago ne ake siyarwa sannan ga dan karan tsada da buri da aka saka wa ragunan.
” Ina ganin idan an dan karya farashin su za a siya, sai dai kila ba kamar yadda a ke so ba.
A garin Enugu ma, ‘yan kasuwa sun ce abin na kama bara ba.
” Idan aka duba yadda aka ta yin rubi in raguna a sallar bara, bana ba a sami haka ba. Muna nan muna jiran masu layya, su zo su siya raguna.
Su ko mutanen garin Hadejia, Karanci ragunan aka samu. Mutanen gari sun bayyana cewa, a dalilin karancin da aka samu sun yi tashin gwajron zabi.
” Bayan masu siyan ragunan domin layyah, mutanen da suka rasa dabbobin su a ambaliyar da aka yi a kauyukan garin suma sun fito domin siyan dabbobi na kiwo. Duk wadannan na daga cikin abubuwan da ya sa suka yi tsada.