Nan da nan sai ka zama mashahurin attajiri da kiwon Macizai – Abubakar

0

Jami’in dake kula da cibiyar bincike da samar da maganin sarar macizai dake Kaltingo jihar Gombe, Abubakar Ballah ya hori mutanen Najeriya da su rungumi kiwon macizai gadan-gadan.

Abubakar ya bayyana cewa sana’ar kiwon macizai akwai riba matuka sannan nan da nan sai ka ga mutum ya kudance.

Ya ce da dafin maciji ake yin maganin maciji idan ya sari mutum.

” Sannnan bayan haka ana amfani da dafin macijin wajen yin maganin Hawan Jini, Sankara da sauran su.

” Kasar Indonesia ne ke da ma’ajiyar macizai kala-kala mafi girma a duniya. Kuma suna siyarwa kasashen duniya da dama inda suke samun makudan kudin shiga ta haka.

” Ana amfani da fatar maciji wajen yin kayan sawa, jaka, tabarmi da dai sauran su.

” Haka kuma idan aka rangada maka farfesu da naman maciji a wasu kasashen Afrika da Chana, zaka sha kana lashe kwano. Sannan yana taimaka wa raya kasar noma da ingantata.

Ballah ya kara da cewa duk da akwai dan wuya kiwon, maciji yakan gudu wa motsi ne idan ya ji shi amma idan aka takura masa ne yakan nemi kare kan sa.

Share.

game da Author