Mambobin Majalisar Dattawa biyu, Sanata Isa Misau da kuma Sanata Rabi’u Ibrahim, sun jajirce cewa za su mika kudiri a Majalisar Dattawa, wanda zai tilasta wa Gwamnatin Tarayya kafa Kwamitin Bincike kan yadda jami’an SSS suka yi wa majalisar dirar-mikiya, sanye da hulunan da suka rufe fuskokin su
Misau da Ibrahim sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da suka fitar, kuma su biyun suka sa mata hannu.
Sun ce kwamitin binciken zai sa ‘yan Najeriya sanin takamaimen dalilin da ya sa SSS din suka kai mamayar da kuma wadanda ke da hannu a cikin wannan haramtacciyar dirar-mikiya da suka yi.
Sun ce wannan mika kudiri na daya daga cikin ababe masu muhimmanci da za su fara gabatarwa da zaran majalisa ta koma daga hutun da ta ke.
Sun ce. “Abin akwai daure kai, a ce dai har yau Gwamnatin Tarayya ba ta kafa kwamitin binciken wannan fyade da jami’ann tsaro suka yi wa dimokradiyya da rana tsaka. Keta haddin Majalisar Tarayya ai kamar yi wa dimokradiyya juyin mulki ne
Don haka suka ce ba za su bari gwamnatin tarayya a hankada darduma ta boye wannan farmaki da aka kai wa majalisa ba. Sun ce korar Lawan Daura daga shugabancin SSS ba zai magance rikicin ba, sai an yi bincike. A yanzu mu na son yadda za a yi mu raba kan mu da wannan cutar kansa da ke addabar mu ba.
Discussion about this post