Sanata Ubale shittu ya yi mana halacci, Inji mutanen shiyyar Hadejia

0

Dubban magoya bayan sanata Ubale Shittu na jam’iyyar PDP a jihar Jigawa ne suka fito manyan titunan garin Hadejia domin nuna goyon bayan su 100 bisa 100 ga sanatan dake wakiltar shiyyar, Sanata Ubale Shittu.

” Mu dai a wannan yanki, Ubale yayi mana halacci.

Shi dai wannan gangami na maida martani ne ga wanda aka yi a kwanakin baya da wasu suka fito don nuna adawar su ga sanatan.

Idan ba a manta ba a ranar Lahadin da ta gabata ne mutanen garin Hadejia suka yi zangar- zangar nuna kiyayyar su game da ficewar da shi wannan sanatan ya yi daga APC zuwa PDP.

Matasan na kira ne ga sanata Ubale Shittu da ya sauka daga kujerar sanata da yake a kai.

Wadannan matasa sun tako ne wasu da kafa wasu bisa ababen hawa, tun daga masana’antar sarrafa rake dake Hadejia zawa fadar sarkin Hadejia a na kwarara ruwan sama suna raira wakoki suna cewa ‘duk wanda ya ki Buhari barawo ne’,‘Buhari shi ne mai cecen mu daga nan har 2023.’

Matasan sun ce cikin dalilan da ya sa shittu ficewa daga APC zuwa PDP sun hada da rashin jituwar dake tsakanin sa da gwamnan jihar Mohammed Badaru. Domin ya sha yin barazana sai ya tsige gwamna Badaru daga kujerar gwamnan jihar Jigawa.

Sannan kuma wai Shittu ya yanke hukuncin haka ba tare da ya yi shawara da mutanen mazabar sa ba da haka ya sa suka yi masa bore.

‘‘Mu muka bashi sharawar ya fice daga APC ya koma PDP saboda gwamna Badarau ya kasa cika alkawarin sa tun da ya hau mulki.

‘‘Kafin zaben 2015 mun fito mun mara wa Badarau da shugaban kasa Muhammadu Buhari baya da sa ran cewa za su biya mana bukatun mu amma tun da suka hau mulki shuru ka ke ji.

Usman ya kuma ce Badarau macuci ne domin tun da ya zama gwamnan babu wani abin a zo a gani da ya yi a masarautar Hadejia.

“Ayyukan da gwamna Badarau yake kadamar wa a garin duk na gwamnatocin baya ne.

Usman ya ce tabbas sa sun doka Badara da da kasa a 2019.

A karshe kakakin Badarau, Bello Zaki a na shi tsokacin yace Shittu neman magana kawai yake yi a jihar Jigawa domin babu wani yanki a jihar da ta fi more wa wannan gwamnati kamar yankin Hadejia.

Share.

game da Author