Sojojin sun kashe mahara biyar a dajin Birnin Gwari

0

Rundunar Sojojin Bataliya ta 1 da ke Kaduna, ta bada sanarwar kashe mahara biyar a dajin Birnin Gwari, sannan kuma ta kwaro makamai a hannun maharan.

Sanarwar ta kara da cewa soja daya ya rasa ransa yayin gumurzun da suka yi da ‘yan bindigar a Birnin Gwari, cikin jihar Kaduna.

Mataimakin Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na rundunar sojojin, Mohammed Dole ne ya bayyana haka a cikin wani bayani da ya fitar yau Alhamis a Kaduna.

Dole ya kara da cewa sojojin sun kai agajin gaggawa ne yayin da aka sanar da su cewa ‘yan fashi da makami sun tare hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua.

Ya ce a lokacin da suke fafutikar neman ‘yan fashin, sai kawai mahara suka yi musu kwanton-bauna, sai dai sun ci karfin maharan tilas suka tsere suka shige cikin Dajin Kuyambana da ke jihar Zamfara.

Ya ci gaba da cewa da suka tsananta bin maharan, sun tsinci gawar biyar daga cikin wadanda suka harba a batakashin da suka yi.

Daga cikin wadanda aka kashe din, Dole ya ce har da wani hatsabibin da ake kira Sani Danbuzuwa.

Share.

game da Author