Idan ba a manta ba a kwanakin bayan ne kasuwar saida gwanjo dake Taminus a garin Jos ta babbake kurmus a sanadiyyar gobarar wuta da aka yi a kasuwar.
‘Yan kasuwan dake kai komo a kasuwar sun fara komawa kangon shagunan su da suka kone domin ci gaba da kasuwancin su.
A jiya Laraba, kasuwar ta cika fam da masu siye da siyarwa ana ta hada-hada da cinikayya.
Duk da cewa gwamnati ta gargadi ‘ya. Kasuwan da kada su kuskura su koma sai an gina musu wani, sun yi watsi da haka abin su.
A halin da ake ciki, yan kasuwan sun ce sun gaji da jiran gwamnati ne shine yasa suka koma cikin kasuwar hakanan.
Sai dai kuma gwamnati ta tura jami’an tsaro zuwa wannan kasuwa domin fatattakar wadannan ‘yan kasuwa, cewa akwai hadari a komawar da suka yi, ba a gina sabuwar kasuwa ba.