Za a gina dakunan bahaya Miliyan 20 a jihar Kano

0

Gwamnatocin jihar Kano da na Tarayya sun rattaba hannu a takardar yarjejeniyar samar da ruwan sha da ayyukan tsaftace muhalli a jihar Kano.

Ministan ruwa Suleiman Adamu ya sanar da haka a Abuja inda ya kara da cewa za a kashe Naira biliyan 12.7 a wannan shiri sannan za’a dauki shekara 15 kafin a kammala aikin.

Ya ce gwamnatin za ta hada hannu da masu ruwa da tsaki a jihar don ganin an sami nasarar kammala wannan shiri a jihar.

Adamu ya ce shirin ya kunshi gyara fanfunan ruwa da rijiyoyin burtsatse 77,693 sannan kuma za a gina wasu sabbi guda 17,264 a yankunan karkara.

Ya kuma kara da cewa za a gina dakunan bahaya 20,600,000 daga farkon shekarar 2019 zuwa 2025 domin sama wa mutane wuraren bahaya a jihar.

A nashi tsokacin, gwamna Abdullahi Ganduje ya ce amincewa da wannan shiri da gwamnatocin biyu suka yi ya nuni ne na ganin an inganta rayukan mutanen jihar da wannan gwamnti tasa a gaba. Sannna kuma gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan 32 a kasafin kudin ta na shekarar 2018 domin samar wa mutanen jihar da tsaftattacen ruwa.

Share.

game da Author