Gwamnatin jihar Kebbi ta bayyana cewa zata biya ma’aikatan jihar albashin watan Agusta saboda shagulgulan Babban Sallah.
Mai taimaka wa gwamnan jihar kan harkokin yadda labarai Abubakar Dakingari ya sanar da haka wa manema labarai a Birnin Kebbi.
Ya kara da cewa gwamnati ta yi haka ne domin kara wa ma’aikatan jihar zamma da kuma sa su maida hankali a wajen aikin su.
Gwamna Atiku Bagudu ya hori mutanen jihar da su yi amfani da wannan lokacin na Eid-el-Kabir domin yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a da samun zaman lafiya a kasa Najeriya.
Discussion about this post