An bude fannin kula da masu cutar zazzabin lasa a asibitin Enugu

0

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Enugu Fintan Echochin ya bayyana cewa jihar ta bude sashen kula da wadanda suka kamu da cutar zazzabin lasa a asibitin koyarwa na jami’ar Enugu.

Echochin ya fadi haka ne ranar Talata a garin Enugu inda ya kara da cewa gwamnati ta bude wannan sashe ne ganin cewa ana bukatar haka.

Ya ce idan ba a manta ba a makon da ta gabata ne wani ya rasu sanadiyyar kamuwa da wannan cuta a asibiti.

Ya ce a dalilin haka gwamnati ta gaggauta daukan matakai domin dakile yaduwar cutar da a yanzu haka ya sa dole a bude irin wannan sashe.

” Bincike ya tabbatar mana cewa babu wanda ya shigo mana da wannan cuta jihar mu kuma duk ‘yan uwa da sauran mutane da wannan mamaci ya yi hulda da basu kamu da cutar ba, bayan gwaji da muka yi.

Ya kuma kara da cewa gwamnati ta horas da mutane domin bin gida-gida suna wayar da kan mutane game da cutar.

Share.

game da Author