Buhari bai kara kwanakin hutun sa a Landan ba – Fadar Shugaban Kasa

0

Fadar Shugaban Kasa ta karyata labarin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya kara wa’adin hutun sa na kwanaki 10 da ya ke yi a Landan, cewa labarin karya ce.

Shafin twitter mallakar Fadar Shugaban Kasa a cikin daren jiya Talata ta karyata labarin, ta na cewa wanda aka buga a jiya, tsohon labari ne tun na ranar 4 Ga Fabrairu, 2017 a lokacin da ya je hutu cikin waccan shekarar.

Fadar ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da labarin cewa karya ne.

“Mu na kiran ‘yan Najeriya da su yi watsi da labarin, su yi la’akari da ranar da kuma shekarar, tun 2017 ce, domin Shugaba Buhari bai kara kwanakin hutun da ya ke yi a Landan ba.”

A jiya ne dai labari ya yadu cewa Buhari ya rubuta wa Majalisar Tarayya wasikar sanarwar kara kwanakin hutun da ya ke yi a Landan.

Buhari ya ce kwanaki 10 zai yi a Landan, amma tun a ranar 3 Ga Agusta ya fara hutu.

Wannan na nufin Buhari zai kammala hutun sa a ranar Juma’a, 17 Ga Agusta, 2018 kenan.

A ka’idar aikin gwamnati, ba a lissafa ranakun Asabar da Lahadi a cikin ranakun da ma’aikaci ya dauki hutu.

Duk lokacin da Buhari ya tafi hutu ko jinya, Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo kan dauki wasu matakan gaggawa, a kan batutuwan da Buhari kan kauda kai, duk kuwa da irin kiraye-kirayen da ake yi masa na ya gaggauta daukar mataki.

Cikin makon da ya gabata Osinbajo ya tsige shugaban SSS na lokacin, Lawal Daura, dan garin su Buhari. Jiya Talata kuma ya umarci Sufeto Janar na ‘yan sanda, Ibrahim Idris, da ya gaggauta yi wa rundunar ‘yan sandan SARS garambawul.

Dalili kenan sau da yawa idan Buhari ba ya kasar, har shagube da gwasale shi akan yi, ana yabon Osinbajo, shi kuma Buhari ana cewa Allah ya sa ya kara kwanaki bai dawo ba.

Share.

game da Author