Hukumar Gudanarwar Shirya Wasannin Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta duniya, ta furta cewa daga yau Talata zuwa ranar Litinin mai zuwa, za ta dakatar da Najeriya, muddin ta ki bin umarnin hukumar.
FIFA ta bayyana haka a cikin wani jawabi da ofishin hulda da kafafen yada labarai na hukumar ya fitar a yau Talata, inda ta ce ta na bibiyar abin da ke faruwa a cikin harkokin kwallon kafar kasar, kuma ta damu irin yadda gwamnatin kasar ke yi na shiga harkokin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya.
Ta ce dole ne Najeriya ta tabbatar da Amaju Pinnick ya shiga ofishin sa na Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, nan da zuwa ranar Litinin mai zuwa.
Sai dai kuma FIFA ta kara sa cewa duk ma irin tsatstsauran matakin da za ta dauka, to ba zai shafi kungiyar Kwallon Mata ‘Yan Kasa da Shekaru 20 da a yanzu ke cikin gasar cin Kofin Duniya a Faransa.
Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya ruwaito rikici ya kai har ofishin Hukumar Kwallon kafa a Najeriya ya na kokarin komawa a hannun mutane biyu, ana ja-ni-in-ja-ka da ba-ni-in-ba-ka, a tsakanin masu jayayyar biyu.
Yayin da gwamnati ko Ma’aikatar Harkoki Wasanni ta Kasa ke bayan Chris Giwa, ita kuwa FIFA ta tsaya tsayin daka cewa Amaju ta sani a matsayin shugaba.
Discussion about this post